Najeriya

Yunkurin kafa rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya

Sifeto Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris
Sifeto Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris THISDAYLIVE

Babban sufeton ‘yan Sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya ce lokaci bai yi ba da za’a kafa rundunar ‘Yan Sandan Jihohi domin samar da tsaro, ganin irin matsalolin siyasar da ake fuskanta.

Talla

Idris wanda ke gabatar da kasida ga taron gwamnonin jihohin kasar da suka kafa kwamitin domin nazarin bukatar haka, ya ce ganin irin yanayin siyasar da kasar ke ciki da kuma fargabar yadda masu mulki za su iya yin amfani da ‘yan Sandan wajen musguna wa abokan hamayya, a ganinsa lokacin bayar da damar fara amfani da wannan tsari a jihohi bai yi ba.

Sufeton ‘yan sanda ya bukaci inganta rundunar da ake da ita a yanzu wajen taimaka ma ta da kayan aiki da kuma isassun kudade domin aiwatar da aikinta.

Tuni Gwamnonin Jihohin suka kafa kwamitin mutane shida domin ba su shawara kan kafa rundunar a matakin Jihohi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.