Nijar

Amurka ta ba da dala milyan 45 don taimaka wa 'yan gudun hujira a Nijar

'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Jihar Diffa
'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Jihar Diffa irinnews.org

Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijar gudunmuwar dala milyan 45 domin taimaka wa dubban ‘yan gudun hijirar Boko Haram da ke zaune a cikin jihar Diffa da ke gabashin kasar.

Talla

Sanarwar da ofishin Hukumar Agajin Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Yamai ya fitar, wanda shi ne zai tafiyar da wadannan kudade, ta ce za a yi amfani da tallafin ne domin daukar dawainiyar dubban ‘yan gudun hijirar wadanda suka tsere wa rikicin Boko Haram daga Najeriya domin samun mafaka a yankin na Diffa da ke Nijar.

A cikin watan yulin da ya gabata ne kasar Nijar ta bukaci kasashen duniya da su taimaka da kudade domin daukatar dawainiyar ‘yan gudun hijirar wadanda yawansu ya kai dubu 150.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.