Najeriya

Ana zaben kananan hukumomi a jihar Lagos

Akwatin zabe a Najeriya
Akwatin zabe a Najeriya http://nigeriannewsdirect.com

A wannan asabar ana gudanar da zaben kananan hukumomi a Lagos, jihar da ta fi kowace yawan jama’a a tarayyar Najeriya, zaben da ake kallo a matsayin babban kalubale ga jam’iyyar APC da ke mulki a jihar da kuma matakin tarayya.

Talla

An dai baje dimbin jami’an tsaro tare da takaita zirga-zirgar jama’a a duk tsawon yinin yau, lura da irin yadda aka gudanar da zazzafan yakin neman zabe a tsakanin ‘yan takara da suka fito daga jam’iyyun siyasa bambamta.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandar jihar ta Lagos ASP Olarinde Famous-Cole, ya ce sun kama mutane da dama da ake zargi da karya doka, da suka hada daukar makamai da dai sauransu.

Ana gudanar da zaben na yau ne a cikin kananan hukumomi 20 daga cikin 37 da ake da shi a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.