Najeriya

Dalilan da suka sa soji kai hari kan sansanin 'yan gudun hijira

Rundunar sojin saman Najeriya na shirin kwashe 'yan matan Chibok da aka ceto don mika s ga iyayensu
Rundunar sojin saman Najeriya na shirin kwashe 'yan matan Chibok da aka ceto don mika s ga iyayensu Bilyaminu/RFIHausa

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa taron da mutane suka yi irin na ba zata a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke cikin jihar Borno, shi ne babban dalilin kai harin soji ta sama a kan kuskure har aka samu asarar rayukan mutane 112 a ranar 17 ga watan janairun da ya gabata.

Talla

Har ila yau sanarwar da Manjo janar John Enenche, mai maigana da yawun ma’aikatar tsaron kasar ya fitar ta ce sansanin da aka kafa a Kala-balge, ba ya daga cikin wuraren da aka sanar da sojoji a matsayin matattarar ‘yan gudun hijira, abin da ya sa aka kai hari kansu akan kuskure.

Da farko dai an tsara za a fitar da rahoton bincike dangane da dalilin faruwar wannan kuskure ne tun a cikin watan fabarairun da ya wuce, to amma sai bayan watanni shida aka fitar da rahoton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.