Najeriya

Saudiyya ta taso keyar 'yan Najeriya zuwa gida

Jirgin sama
Jirgin sama

Mahukuntan Saudiyya sun taso keyar ‘yan Najeriya da yawansu ya kai 198, da ke zaune a kasar ba a kan ka’ida ba, wadanda aka sauke a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da misalin karfe 10 na safiyar yau asabar.

Talla

Jami’an hukumar agajin gaggawa ta kasar NEMA ne suka karbi mutanen wadanda cikinsu akwai maza da mata, wadanda karamin jakadan Najeriya a birnin Jeddah na Saudiyya ya yi wa jagora har zuwa gida.

Ba wannan ne karo na farko da mahukuntan Najeriya ke cafkewa tare da taso keyar 'yan Najeriya da ke zaune kasar ba a kan ka'ida ba, kuma mafi yawansu na fakewa bayan kammala aikin hajji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI