Nijar

Tallafin Amurka zuwa yan gudun hijira na Diffa

'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Jihar Diffa
'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Jihar Diffa AFP PHOTO/OLATUNJI OMIRIN

Amurka ta ware milyan 45 na dala kwatakoncin Euros milyan 39 a matsayin taimako zuwa yan gudun hijira da mutanen da rikicin boko haram ya tilasatawa kasancewa yan gudun hijira a yankin Diffa dake kudu maso gabacin kasar.

Talla

Wadanan kudade za su taimakawa domin samarwa yan gudun hijirar abinci mai gina jiki, banda haka kungiyoyi ma su aiki a wannan yankin za su samu kwari guiwa wajen gudanar da ayyukan.

A watan yulin shekarar 2016 ne gwamnatin Nijar ta shigar da bukata na tattaro kudade daga kasashen waje domin kai dauki zuwa mutanen da rikicin Boko Haram ya ritsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.