ECOWAS ta bukaci daukar matakin kayyade haihuwa
Wallafawa ranar:
Wakilan kungiyar kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS, sun bukaci da dauki matakin rage yawan haihuwa a yankin, domin kaucewa samun yawan al’umma fiye da kima.
Kakakin majalisar kasar Burkina Faso, Salifou Diallo, ya ce akwai bukatar rage yawan hayayyafar da ake samun a yammacin na Afrika da akalla rabi na da zuwa shekara ta 2030, idan akai la’akari da cewa yankin kan gaba a duniya da aka fi samun haihuwa.
A cewarsa kamata yayi a ce an kayyade haihuwar yara 3 kawai ga ko wace mace domin cimma wannan buri.
Wani rahoton majalisar dinkin duniya ya yi hasashe cewa zuwa shekara ta 2050 yawan jama’a a yammacin nahiyar Afrika kadai, zai kai akalla biliyan 1, kasancewar akalla kowace mace a yankin na iya haihuwar yara 6.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu