Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo

Jamhuriyyar Congo: 'Yan adawa sun bai wa Kabila wa'adi

Shugaban Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo Joseph Kabila, a babban birnin kasar Kinshasa.
Shugaban Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo Joseph Kabila, a babban birnin kasar Kinshasa. REUTERS/Kenny Katombe

Gamayyar jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Kongo sun cimma matsayar daukar wasu jerin matakai, domin tilastawa shugaban kasar Joseph Kabila, sauka daga mukaminsa.

Talla

Sanarwar ta zo ne bayan kammala taron kwanaki biyu tsakanin wakilan ‘yan adawar kasar a birnin Kinshasa, inda suka tattauna kan zaman dirshan da Kabila ke cigaba da yi a kujerar shugabancin kasar tun daga shekarar 2001.

Mai magana da yawun ‘yan adawar Francois Muamba, ya ce, a ranar 8 ga watan Agustan mai zuwa, zasu gudanar da yajin aikin gama gari na tsawon kwanaki 2, a mtsayin gargadi, yayinda kuma a ranar 20 ga watan ma Agusta za’a gudanar da zanga-zanga a birnin Kinshasa da sauran lardunan kasar 25.

Muamba ya kara da cewa idan har kabila ya cigaba da zama a kujerar shugabancin kasar, har zuwa karshen watan Satumba kuwa, to fa daga ranar 1 ga watan Oktoba zasu daina daukarsa a matsayin shalataccen shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI