Cote d'Ivoire

Jami'an Tsaron Cote d'Ivoire Sun Dakile Wani Hari Kusa Da Birnin Abidjan

Wasu Sojan kasar Cote d'Ivoire
Wasu Sojan kasar Cote d'Ivoire RFI

Jami'an tsaron kasar Ivory Cote d'Ivoire sun yi ta dauki ba dadi da wasu mahara da suka kai samame a arewacin birnin Abidjan, a wani lokaci da dubban jama’a ke halartan birnin inda aka fara gasan wasanni da na al’adun gargajiya na kasashen dake magana da harshen Faransanci.

Talla

Maharan sun kai samamen ne a daidai garin Azaguie, kwanaki kadan bayan jami'an tsaron kasar sun maida martani ga kwatankwacin irin wannan samame da aka kai kusa da garin na Abidjan.

Wani jami’in tsaro na Jandarma ya bayyana cewa maharan cikin dare suka diramma wata gada dake garin na Azaguie, amma kuma ba’a sami hasarar rai ba.

Za'a kwashe kwanaki 10 ne ana gasan wasannin na kasashen duniya kusan 50 dake magana da harshen Faransanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI