Africa

Wani yaro ya warke daga Cutar Kanjamau

Rayuwar miliyoyin masu fama da cutar kanjamau a duniya dai ta ta'allaka kan kwayoyin rage kaifin cutar na antiretroviral drug
Rayuwar miliyoyin masu fama da cutar kanjamau a duniya dai ta ta'allaka kan kwayoyin rage kaifin cutar na antiretroviral drug AFP/Kerry Sheridan

A yayin da masana cutar kanjamau ke gudanar da taron su a birnin Paris domin nazari kan yadda za’a magance cutar da ke ci gaba da lakume dimbin rayuka, wani yaro da aka Haifa a kasar Afirka ta kudu da cutar ya bai wa masana mamaki wajen ganin ya rabu da ita.

Talla

Rahotanni daga Afirka ta kudu sun ce masu fama da cutar kanjamau kan dogara ne da shan maganin da ke rage radadin cutar da ake kira ‘antiretroviral drug’ har iya rayuwar su, amma wannan yaro da ke da shekaru 10 yanzu haka ya dai na shan maganin, kuma babu alamar cutar tattare da shi.

Samun saukin yaron dama wasu irin sa da suka rabu da cutar, sun haifar da fatar cewar mutane miliyan 37 da ke dauke da cutar a duniya na iya samun maganin da za su rabu da ita.

Sai dai masana sun bukaci taka-tsan-tsan kan rahotan, inda su ke cewa ba dole ne yanayin da yaron ya samu kan sa ya kasance daya da sauran masu fama da cutar ba.

Linda-Gail Bekker, shugabar kungiyar masu yaki da cutar da ke jagorancin taron da ake gudanarwa a Paris, ta bayyana nasarar da yaron ya samu a matsayin fata mai kyau na cewar nan gaba masu fama da cutar na iya samun maganin ta ba tare da shan magunguna har iya rayuwar su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI