Libya

Ana zargin dakarun Libya da kashe mutane

Dakarun  Libya masu biyayya ga Janar Haftar
Dakarun Libya masu biyayya ga Janar Haftar MAHMUD TURKIA / AFP

Kungiyoyin Kare hakkin Bil Adama sun bukaci gudanar da bincike kan wani faifan bidiyo dake nuna yadda sojojin kasar suka kashe wasu mutane 20 da ake zargin yan ta’adda ne.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ga bidiyon da ake zargin sojojin dake yiwa kwamanda Khalifa Haftar biyayya suna aikata kisan, sai dai bashi da tabbacin sahihancin sa.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi da dama sun gargadi baki da su kaucewa zuwa kasasr Libya saboda yadda ake azabtar da mutane da kuma hallaka su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.