Birtaniya-Guinea

Birtaniya zata kaddamar da bincike a Guinea

Ofishin binciken manyan laifufukan Birtaniya ya kaddamar da bincike kan katafaren kamfanin hakar ma’adinan Rio Tinto dake aiki a kasar Guinea saboda zargin cin hanci.Shirin kamfanin na hakar ma’adinin karfe a kasar Guinea ya gamu da zargin cin hanci, abinda ya haifar da daukar matakan shari’a.

Man feutr a kasar Guinea
Man feutr a kasar Guinea
Talla

Kamfanin da kan sa ya gurfanar da kan sa a gaban masu bincike a karshen shekarar bara, bayan binciken cikin gida ya gano cewar an bada cin hancin kudi sama da Dala miliyan 10 ga jami’an gwamnati dan samun damar gudanar da aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI