Faransa- Italya-Libya

Faransa na kokarin sasanta yan Libya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Reprodução de vídeo

Takaddama ta kaure tsakanin Faransa da Italya kan yunkurin sasanta rikicin kasar Libya wadda ta fada cikin tashin hankali tun bayan kawar da shugaba Mua’ammar Ghadafi daga karagar mulki.

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shirya wata ganawa yau talata tsakanin sa da shugabannin bangarorin da basa ga maciji da juna a Libya, sai dai matakin bai yiwa Italya dadi ba, wadda tace ana neman mayar da ita saniyar ware.

Yan siyasar Italya na kallon yunkurin na Macron a matsayin gazawar Firaminista Paolo Gentilino.

Gentilino ya bayyana fatar samun nasara kan sabon yunkurin na Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.