Tallafi zuwa yan gudun hijira a Diffa
Wallafawa ranar:
Amurka ta bayyana bada tallafin dalla milyan 45 domin tallafawa yan gudun hijirar rikicin boko haram a yankin Diffa dake kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar, kan iyakar kasar da tarayyar Najeriya, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta sanar
A karshen watan yulin shekarar bara ne dai, gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bukaci kasashen duniya da su tallafawa hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya PAM da kudi, bayyan da hukumar ta bayyana cewa zata dakatar da ayyukan tallafin da take ga yan gudun hijirar saboda rashin kudi.
To sai dai tuni masu sharhi kan ayyukan jinkai a kasar na bukatar ganin an zura ido sosai ta yadda tallafin zai kai ga mabukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu