Mata sun yi zanga-zangar sakamakon tsanantar fyade a Kano
Wallafawa ranar:
Daruruwan matan aure da zaurawa ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Kano da ke Najeriya domin ganin nahukunta sun dauki matakai masu tsauri kan mutanen da ke yi wa mata da kanana yara fyade.
Wannan dai wata babbar matsala ce da ke ci gaba yin kamari a jihar ta Kano a daidai lokacin da jama’a ke ganin cewa mahunka ba sa daukar matakan da suka dace domin magance matsalar.
Wakilinmu a Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya ce a cikin shekara daya kacal an samu rahotannin aikata fyade fiye da sau 700 a cikin jihar, lamarin da ya janyo hankalin kungiyar tsoffin daliban makarantar St-Louis shirya zang-zangar ta ranar talata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu