Najeriya

Gwamnonin PDP sun gana da Buhari a birnin London

Gwamnonin Najeriya tare da shugaba Muhammadu Buhari a birnin London
Gwamnonin Najeriya tare da shugaba Muhammadu Buhari a birnin London RFIHAUSA/Bashir

Tawagar gwamnonin Najeriya ta gana da shugaban kasar Mahammadu Buhari da ke jinya a birnin London na kasar Birtaniya a wannan laraba.

Talla

Tawagar ta kasance ne a karkashin jagorancin shugaban taron gwamnonin Najeriya Abdul Aziz Yari, gwamnan jihar Zamfara.

Sauran gwamnonin da tawagar ta kunsa sun hada da Abdullahi Ganduje na Kano da Kashim Shettima na Borno da Samuel Ortom na Benue da Udom  Emmanuel na Akwa Ibom da  Abiola Ajimobi na Oyo da kuma Dave Umahi na Ebonyi.

Shugaba Buhari ne ya bai wa gwamnonin damar kai ma sa ziyara kamar dai yadda Garba Shehu, mai magana da yawunsa, ya shaida wa sashen hausa na RFI.

Sai dai kawo yanzu cikakken bayani kan abin da gwamnonin suka gana da shugaba Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI