Najeriya

Dangote ya koma na 105 a sahun attajiran duniya

Attajirin Afrika Aliko Dangote na Najeriya
Attajirin Afrika Aliko Dangote na Najeriya (cc) Wikimedia/World Economic Forum

Attajirin Afrika Aliko Dangote na Najeriya ya koma matsayi na 105 daga  matsayi na 51 a jerin attajiran duniya, kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa.

Talla

Mujallar ta ce faduwar darajar kudin Najeriya ya sa arzikin Dangote ya ragu daga dala biliyan 15.4 a bara zuwa biliyan 12.6 a bana.

A bara ma Dangote ya yi hasarar kashi sama da 35 na arzikinsa sakamakon faduwar darajar Naira akan dalar Amurka.

Najeriya dai ta fada cikin matsalar tattalin arziki ne sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya, kuma wannan ne ya shafi darajar kudin kasar.

Dangote wanda kasuwancinsa ya shafi kayan abinci da siminti, yanzu kuma ya fado cikin harakar fetir inda yanzu haka ya ke aikin gina matatar mai a Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.