Najeriya

An umurci manyan hafsoshin tsaron Najeriya su koma Maiduguri

Babban kwamandan sojin kasan Najeriyta, Janar Tukur Buratai
Babban kwamandan sojin kasan Najeriyta, Janar Tukur Buratai AFP PHOTO/STRINGER

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osibanjo ya umurci shugaban rundunar sojin kasa Janar Tukur Burutai da shugaban sojin sama Sadiq Abubakar da su koma Maiduguri domin magance matsalar tsaron da ake ci gaba da samu a yankin.

Talla

Matakin ya biyo bayan ganawar da shugaban ya yi ne da hafsoshin tsaron kasar kan harin da aka kai Maiduguri wanda ya yi sanadiyyar kashe wani Kaftin na soja da wasu mutane 9 cikinsu har da malaman jami’ar Maiduguri, yayin da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewar wadanda suka mutu sun kai 50.

Jami’ar Maiduguri ta tabbatar da kashe wasu ma’aikatanta a harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wa masu binciken man fetur a Magumari da ke cikin jihar Borno a Najeriya.

Shugaban Malaman Jami’ar Maiduguri Dr Dani Mamman ya ce har ya zuwa yanzu ana neman wasu ma’aikatan jami’ar da ba a san halin da suke ciki ba biyo bayan wannan hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.