Zimbabwe

Babu Wani Dalili Da Zan Ajiye Mulki- Inji Robert Mugabe

Shugaba Robert Mugabe na Ziumbabwe cikin wani hoto da aka dauka a Harare ranar 12 ga Aprilu, 2017.
Shugaba Robert Mugabe na Ziumbabwe cikin wani hoto da aka dauka a Harare ranar 12 ga Aprilu, 2017. Jekesai NJIKIZANA / AFP

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana cewa babu abinda zai sa ya ajiye mulkin kasarsa haka kawai, domin bai ga dalilin yin haka ba.

Talla

Robert Mugabe mai shekaru 93 na wadannan kalamai ne yau Asabar a lokacin da yake yiwa magoya bayansa lacca a garin Chinhoyi inda nan ne kauyensa na usuli.

Ya bayyana cewa hatta likitoci na mamakin juriyarsa duk da yawan shekaru da yake da su a duniya.

A dan tsakanin nan Uwargidan Shugaba Mugabe ta nemi mijin nata da ya sanar da duniya wanda yake bukata ya maye kujeransa idan ya sauka daga mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.