Lesotho

An Gano Wasu Naurorin Nadar Magana Makale a Ofishin Firaministan Lesotho

Firaministan Lesotho Thomas Thabane
Firaministan Lesotho Thomas Thabane RFI

Hukumomin kasar Lesotho na bincike musabbabin dasa wasu naurorin nadar magana na sirri da aka dasa a ofishin Firaministan kasar Thomas Thabane a farkon wannan mako mai karewa.

Talla

Kakakin Gwamnatin kasar Thabo Thakalekoala ya bayyanawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa an gano naurorin ne karkashin teburin Firaministan jikin layin wayansa na ofis.

Makonni shida ke nan da shigansa ofis bayan nasarar da jam’iyar sa ta yi a zaben watan jiya.

Ya yi Firaminista tsakanin shekara ta 2012 har daga bisani a shekara ta 2014 ya tsere saboda zargin sojan kasar na neman kashe shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI