Najeriya- Liberia

Najeriya Za Ta Tura Dakaru 230 Kasar Liberia Don Aikin Zaman Lafiya

Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya Tukur Yusuf Buratai RFI

Babban Hafsan Hasoshin Sojan Najeriya Tukur Buratai ya sanar da cewa Najeriya za ta tura Dakarun ta  230 zuwa kasar Liberia don ayyukan wanzar da zaman lafiya.Daga ciki 19 manya ne yayin da 211 masu kananan mukamai ne.

Talla

Janar Tukur Buratai na magana ne a Kaduna yayin rufe horas da Dakarun na makonni hudu game iya jagoranci da kwarewa wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Ya bukaci Dakarun da aka horas da su kasance masu halayen kirki ba wadanda za su bata sunan Najeriya ba a kasar da za su.

Ya bayyana cewa daga shekara ta 1960 zuwa yanzu Najeriya ta tura Dakarunta dubu ashirin zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya sau 40 a kasashen Africa da wasu kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI