Kenya

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Mataimakin Shugaban Kasar Kenya William Ruto

A kasar Kenya wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan Mukaddashin Shugaban kasar William Ruto yau Asabar, makonni kasa da biyu kafin babban zaben kasar mai cike da rudani.

Uhuru Kenyatta Shugaban Kenya da kuma  Raila Odinga jagoran adawa
Uhuru Kenyatta Shugaban Kenya da kuma Raila Odinga jagoran adawa RFI
Talla

Majiyoyin samun labarai sun shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa an kai wannan hari ne a lokacin da Mukaddashin Shugaban kasar ba ya cikin gidan, kuma har an jikkata wani jami’in tsaro mai gadi.

Wani jami’in Gwamnati ya gaskata cewa an kara jibge jami’an tsaro a gidan Mukaddashin Shugaban sannan kuma ana ci gaba da gudanar da binciken lamarin.

Shugaba Uhuru Kenyata wanda William Ruto ke yi wa mataimaki za su sake fafatawa ne a babban zaben kasar ranar takwas ga watan gobe da tsohon dan adawa Raila Odinga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI