An fara jigilar alhazzan Najeriya
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da alhazzai a Najeriya ta fara aikin jigilar maniyata zuwa kasar Saudiya domin gudanar aikin hajjin bana. An fara jigilar alhazzan Abuja ne a yau Lahadi zuwa Madina.
Jirgin Flynas ne na Saudiya ya fara aikin jigilar Alhazzan daga filin Nnamdi Azikwe na Abuja.
Sauran jiragen da za su ci gaba da aikin jigilar alhazzan sun hada da Azman da Max Air.
Hukumar alhazzan ta Najeriya ta ce kimanin maniyata 79,000 ne ta yi rigista domin aikin hajjin bana daga jihohin kasar 36 hadi da Abuja.
A lokacin kaddamar da tashin alhazzan a bana, Ministan Abuja Muhammad Bello wanda ya wakilci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bukaci Alhazzan su kaucewa dabi’un da za su bata sunan Najeriya tare da kasancewa cikin tsoron Allah a yayin da suke gudanar ibadar Hajji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu