Kamaru

Shekaru biyu Ahmed Abba na tsare a Kamaru

Ahmed Abba, wakilin RFI Hausa a yankin Arewacin Kamaru
Ahmed Abba, wakilin RFI Hausa a yankin Arewacin Kamaru www.rfi.fr

A yau Lahadi shekaru biyu cur ke nan wakilin RFI Hausa a Kamaru Ahmed Abba na tsare a gidan yari, a yayin da ya ke jiran hukuncin karar da ya daukaka bayan yanke masa hukuncin daurin shekaru 10.

Talla

Kotun sojin Kamaru ce ta yanke wa Ahmed Abba hukunci bayan tuhumarsa da taimakawa ayyukan ta’addanci a aikinsa na jarida, laifin da babu hujjoji akan dan jaridar da ke aiko wa sashen Hausa na RFI da rahotanni daga yankin arewa mai nisa.

Kungiyar ‘yan jaridu ta duniya Reporters Without Borders ta yi allawadai da ci gaba da tsare wakilin na RFI Hausa.

Kafin yanke masa hukunci Abba ya shafe watanni a tsare cikin yanayi na wahala da azabtarwa tun watan Yulin 2015 da aka kama shi a yankin arewa mai nisa.

A cikin wata sanarwa, sakataren kungiyar ‘yan jaridun Janar Christophe Deloire ya ce babu dalilin da za a ci gaba da tsare Abba.

Hukumomin RFI sun dade suna allawadai da kama ma'aikacin na sashen Hausa ba tare da Kamaru ta gabatar da hujjojin dalilin tsare shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.