Kaduna

An tarwatsa taron su Shehu Sani a Kaduna

Wasu ‘yan daba sun tarwatsa taron manema labarai da Jam’iyyar APC bangaren su Sanata Shehu Sani suka kira domin nuna adawa da zaben wakilan Jihar da aka zaba domin wani babban taron Jam’iyyar na kasa.

An tarwatsa taron manema labarai da su Shehu Sani suka kira a Kaduna
An tarwatsa taron manema labarai da su Shehu Sani suka kira a Kaduna RFIHausa/Aminu Kaduna
Talla

Bayanai sun ce Sanata Shehu Sani da Sulaiman Hunkuyi ne suka kira taron manema labaran a ofishin kungiyar ‘yan jaridu a Kaduna domin yin watsi da zaben wakilan Jam’iyyar APC da aka zaba.

Sanatocin sun zargi gwamnatin Malam Nasir El Rufai da alhakin aiko ‘yan bangar siyasa domin tarwatsa taron.

Wakilinmu Aminu Sado da ya halarci taron ya ce akwai dan jaridar kafar Liberty Lawal Muhammad da aka fasa wa kai a wajen taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI