Liberia

Madugun 'yan tawaye da George Weah na cikin 'yan takarar Liberia

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf na gab da kawo karshan wa'adinta
Shugaba Ellen Johnson Sirleaf na gab da kawo karshan wa'adinta REUTERS/Tiksa Negeri

Hukumar zabe a Liberia ta sanar da sunayen mutane 20 da za su yi takarar shugabanci kasar, ciki hadda tsohon madugun ‘yan tawayen kasar Prince Johnson da tsohon dan kwallon kafar duniya George Weah da kuma wata tauraruwar nuna sutira.

Talla

Zaben da zai kawo karshan mulkin shugaba Ellen Johnson Sirleaf da ke tafiyar da kasar a wa’adi na biyu, babu wani dan takara a yanzu da za a ce shine ke kan gaba wajen iya maye gurbinta.

Shugaba Sirleaf da ke mulkin Liberia tun a shekarar 2005 ta yi kokarin farfado da kasar da yakin basasar shekaru ya yi tasiri ga tattalin arzikinta da kuma walwala.

A ranar 10 ga watan Oktober shekarar da muke ciki, ake saran gudanar da zaben da ya hadar da na ‘yan Majalisu da shugaban kasa, kuma wannan shine karon farko tun bayan lafar da kurar rikicin kasar a Shekara ta 2003, za’ayi zabe ba tare da tsaron dakarun wanzar da zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya ba.

Gabanni kaddamar da yakin neman zaben kasar a yau litinnin, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran a gudanar da zaben cikin inganci da kwanciyar hankali, tare da bukatar kowanni bangare ya hada kai wajen gani zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Bayan tiketin da jami’iyun siyasa suka yanka suma manya jiga-jigan kungiyoyin ‘yan tawaye sun shiga sahun gaba, Ciki hada Sanata Prince Johnson, tsohon madugun ‘yan tawaye da ya kashe shugaba Samuel Doe a shekara ta 1990.

Kana akwai Sanata George Weah tsohon dan kwallon kafa a duniya da Jewel-Howard-Taylor matar Charles Taylor za ta yi wa mataimaki.

Sai kuma mace daya tilo da ta shiga sahun mazan da ke takara, MacDella Cooper, tsohuwar tauraruwar nuna sutira da yanzu ke gudanar da ayyukan agaji da raya talaka musamman mazauna karkara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI