Mali

An saki Dan Afrika ta kudu da aka sace a Mali

Stephen McGown, baturen Afrika ta kudu da al Qaeda suka sace a Mali
Stephen McGown, baturen Afrika ta kudu da al Qaeda suka sace a Mali Capture d'écran / Youtube

Ma’aikatar harakokin wajen Afrika ta kudu ta ce an saki wani dan kasar da mayakan Al Qaeda suka sace tun a shekarar 2011 a wata otel a Mali.

Talla

Gwamnatin Afrika ta kudu ta ce babu wasu kudin fansa da ta biya domin sakin mutumin da ya tafi yawon bude ido a Mali

Tuni dai Stephen McGown ya isa gida Afrika ta kudu inda ya hadu da iyalinsa, kamar yadda ma’aikatar harakokin wajen kasar ta tabbatar.

An yi garkuwa da Stephen McGown tare da wasu turawa guda biyu ‘yan kasashen Sweden da Holland a birnin Timbuktu da ke arewacin Mali wadanda tuni aka saka.

Gwamnatin Afrika ta kudu ta yaba wa Tarayyar Afrika da dakarun Faransa da kuma gwamnatin Mali kan rawar da suka taka.

Rahotanni sun ce McGown ya iso cikin koshin lafiya, amma sai an gudanar masa da gwaje gwaje domin tabbatar da koshin lafiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.