DR Congo

DR Congo: An kashe mutane 50 a rikicin kabilanci

Jami'an da ke bada tsaro a DR Congo
Jami'an da ke bada tsaro a DR Congo Mustafa MULOPWE / AFP

Mutane Sama da 50 aka kashe a fadar kabilancin da aka samu a Gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo mai fama da tashin hankali.

Talla

Rahotanni sun ce ‘yan kabilar Twa ne suka kai hari kan ‘yan kabilar Bantu da ke Luba, a tsibirin Tanganyika, abinda ya yi sanadiyar rasa dimbin rayukan.

Bangarorin biyu sun kwashe shekaru da dama suna gwabza yaki a tsakanin su.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya a kasar na ci gaba da bayyana fargaba yadda zaman lafiya ke ci gaba da dakushewa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI