Africa ta Kudu

Zuma ya sake tsallake rijiya da baya

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya sake tsallake rijiya da baya a kuri'ar yankar kauna da Majalisar Dokoki ta kada a sirce a wannan Talata
Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya sake tsallake rijiya da baya a kuri'ar yankar kauna da Majalisar Dokoki ta kada a sirce a wannan Talata REUTERS/Siphiwe Sibeko

Shugaban Afrika Ta Kudu, Jacob Zuma ya sake tsallake rijiya da baya a kuri’ar yankar kauna da mambobin Majalisar Dokokin kasar suka kada a wannan Talata.

Talla

Duk da cewa a karon farko kenan da aka kada kuri’ar a sirce, 'ya'yan jam'iyyar ANC a majalisar sun nuna goyon baya ga shugaba Zuma duk da matsalar rarrabuwar kawuna da ke addabar Jam'iyyar mai mulki.

Ana bukatar kuri’u 201 daga cikin 400 don tisge Zuma amma aka samu kuri’u 177 kamar yadda shugabar Majalisar Dokokin, Beleka Mbete ta sanar jim kadan kammala kuri'ar yankar kaunar .

Gabanin kuri'ar wadda ita ce ta takwas, masu fashin bakin siyasa sun yi hasashen cewa, Zuma zai samu nasara, lura da rinjayen da ANC ke da shi a Majalisar.

Zuma ya samu kuri'a 198 ta goyon baya a gare shi.

Ana zargin shugaban da halasta kudaden haramun da kuma jefa kasar cin matsalar tattalin arziki, abin da ya sa ‘yan adawa ke bukatar tsige shi daga karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.