ECOWAS

Dawo da martabar Amurka a kasuwannin Ecowas

Taron kasashen dake karkashin shirin AGOA
Taron kasashen dake karkashin shirin AGOA AFP PHOTO / Karen BLEIER

Wasu yan kasuwan Amurka zasu ziyarci kasar Togo a cikin wannan mako domin tattaunawa kan matsayin harkokin kasuwancin bai daya tsakanin kasar da kasashen dake Africa ta yamma a karkashin shirin AGOA. Taron da za’ayi tsakanin tawagar ta Amurka da ministocin kasashen dake yammacin Afirka zai mayar da hankali ne kan yadda China ke kokarin mamaye harkokin kasuwanci a wannan yankin da kuma yadda kasar ke bada makudan kudade wajen samar da kayan more rayyuwa a karkashin Bankin zuba jarin Asia.

Talla

A daya wajen Amurka ta fitar da kayan da suka kai Dala biliyan 21 daga Dala biliyan 10 daga shekara ta 2000 kamar yadda ma’aikatar kasuwancin Amurka ta fitar, kasar China ta gudanar da kasuwancin da ya kai sama da Dala miliyan 102 a Yankin Afirka ta yamma a shekarar 2015.

Ana saran tawagar ta Amurka a karkashin Robert Lighthizer ta yi bayani dangane da makomar yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla wadda za ta kare aiki a shekarar 2025, a daya wajen Gwamnatin Donald Trump na kokarin kawo gyara ga wasu daga cikin manufofin da tsohon Shugaban Amurka Obama ya aiwatar a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.