Rwanda

Kagame ya samu kusan kashi 99 na kuri’un zaben Rwanda

Shugaban Rwanda Paul Kagame
Shugaban Rwanda Paul Kagame REUTERS/Jean Bizimana

Hukumar Zabe a kasar Rwanda ta bayyana kamalallen sakamakon zaben shugaban kasar wanda ya nuna cewar shugaba Paul Kagame ya samu kusan kashi 99 na kuri’un da aka kada.

Talla

Alkaluman da hukumar zaben kasar ta gabatar sun nuna cewar bayan Kagame, Frank Habineza na Jam’iyyar Democratic Green Party, ya samu kasa da rabin kashi guda na zaben.

Shi kuma Philippe Mpayimana dan takarar indipenda ya samu sama da rabin kashi guda na kuri’un.

Tuni kasar Amurka da kungiyar kasashen Turai suka bayyana shakkun kan sahihancin zaben.

Shugaba Kagame wanda tsohon shugaban ‘yan tawayen Hutu ne, ya kwashe shekaru 17 a karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.