Najeriya

JAMB ta takaita makin shiga Jami’a zuwa 120

Shugaban hukumar JAMB a Najeriya Is-haq Oloyede
Shugaban hukumar JAMB a Najeriya Is-haq Oloyede JAMB

Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’a da wasu makarantun gaba da Sakandare JAMB ta rage yawan makin jarabawar da sai dalibai sun samu kafin samun nasarar ci gaba da karatunsu.

Talla

Hukumar ta rage makin shiga Jami’a zuwa 120 tare da rage makin shiga kwalejojin Ilimi da na fasaha zuwa maki 100.

Hukumar ta sanar da matakin ne bayan kammala wani babban taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimi a Najeriya a ranar Talata, inda aka yi nazari kan matsalar tare da daukar matakin.

Kafin daukar matakin, dalibai sai sun samu makin Jarabawar JAMB 180 zuwa 200 kafin samun shiga Jami’a a Najeriya.

Dalibai da dama sun fadi jarabawar da aka rubuta a bana, inda hukumar tace dalibai sama da budu dari biyar ne kawai suka samu maki 200 cikin dalibai miliyan 1 da dubu dari bakwai da suka zana jarabawar.

Sai dai kuma har yanzu Jami’o’I na damar kara yawan makin ga dalibai fiye da adadin da hukumar JAMB ta kayyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.