Afrika-Lafiya

Mutane milliyan 9 a Afrika na iya mutuwa saboda katse tallafin HIV

Maganin rage kaifin cuta mai karya garkuwar jiki.
Maganin rage kaifin cuta mai karya garkuwar jiki. AFP

Sakamakon wani bincike ya nuna cewa akalla mutane miliyan 9 zasu rasa rayukansu a kasashen Afirka ta kudu da Cote D’Ivoire sakamakon katse tallafin kudaden taimakawa masu fama da cutar kanjamau da shugaban Amurka Donald Trump yayi.

Talla

Wani binciken farko da aka gudanar kan illar janye tallafin da Amurka tayi, ya nunawa masana kimiya cewar matsalar za tafi kamari a kasashen Afirka.

Rahotan yace kashi 19, na manyan mutane a Afirka ta Kudu na dauke da cutar mai karya garkuwar jiki, kuma suna bukatar agajin, sai kuma Cote d’Ivoire mai mutane dubu 460,000.

Masana kimiyar daga kasashen Amurka, Afirka da kuma Turai sun ce muddin ba’a samu sauyi ba, akalla mutane kusan miliyan 2 zasu mutu nan da shekaru 10 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.