Angola

Jam'iyun Adawa A Angola Sun Nemi A Soke Sakamakon Babban Zaben Kasar

Wasu maaikatan zabe a Angola.
Wasu maaikatan zabe a Angola. rfi

A kasar Angola Jam'iyun siyasa na adawa sun daukaka kara game da sakamakon babban zaben kasar da aka yi watan jiya dake cewa jam'iyar dake mulki ce ta MPLA ta yi nasara.

Talla

Jam'iyun adawan sun bukaci Kotun tsarin mulki ta kasar da ta soke zaben domin ba’a yi bisa sharuddan da dokokin kasar suka shimfida ba.

Jam'iyar adawa ta National Union for the Total Independence of Angola, NUTIA  ta jagoranci daukaka  kara a kotun, inda ta gabatar da tarin hujjoji cikin wani akwati.

Ranar Laraba data gabata Hukumar zabe ta bayyana cewa Jam'iyar dake mulki ta lashe kashi  61%  na kuri'un da aka jefa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.