'Yan kasuwa na tsaikun bude shago a Kano

Sauti 10:15
'Yan kasuwa na kai 11 na safe ba su bude shago ba a kasuwar Kano
'Yan kasuwa na kai 11 na safe ba su bude shago ba a kasuwar Kano RFIhausa/Awwal

Shirin Kasuwanci ya yi nazari ne kan yadda 'yan kasuwa ke tsaikun bude shago a garin Kano duk da ikirarin birnin a matsayin cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya. Shirin ya kai ziyara kasuwar Abubakar Rimi a tsakiyar Kano inda 'yan kasuwa da dama sai karfe 11 na safe suke bude shago.