Kamaru

Daukaka karar wakilin sashen Hausa na rfi a Kamaru

Ahmed Abba, wakilin Sashen Hausa na Rfi a Kamaru
Ahmed Abba, wakilin Sashen Hausa na Rfi a Kamaru via facebook profile

Kotu a birnin Yaounde na kasar Kamaru ta dage sauraran karar da lauyan da ke kare wakilin sashen hausa na rfi Ahmed Abba ya daukaka a gabanta, inda yake neman a soke hukuncin daurin shekaru 10 da aka yanke masa.

Talla

A yanzu dai kotun ta bayyana ranar 19 ga watan okotba mai zuwa domin sauraran wannan karar.

Lauyan Ahmed Abba Maitre Charles Tchoungang, y ace suna da fargaba dangane da matakin dage sauraren karar, lura da cewa bangaren mai zargi ne ya bukaci haka.

To sai dai Maitre Tchoungang ya ce suna kwarin gwiwa lura da cewa shugaban kotun ya amince bangaren Ahmed ya gabatar da wasu sabbin shaidu a nan gaba, wadanda zaman kotunan da aka yi a baya ba a amince da su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.