Chadi

An bukaci Idriss Deby ya dau matakai akan miyagun akidu a Chadi

Shugaban Chadi Idriss Déby
Shugaban Chadi Idriss Déby REUTERS/Alain Jocard

Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a kasar Chadi, wadda ke da alhakin tafiyar da lamurran da suka shafi addini da kuma ilmantarwa, ta bukaci shugaban kasar Idris Deby Itno, da ya dauki mataki dangane da yadda wasu da ake kallo a matsayin masu miyagun akidu ke ci gaba da gina wuraren ibada da makarantu a cikin kasar ba tare da amincewar hukumar da alhakin hakan ya rataya a wuyanta ba.

Talla

Matsalar dai na neman zaman ruwan dare a Chadi, lamarin da ya sa ‘yan majalisar suka yi tattaki har zuwa fadar shugaban domin gabatar masa da wannan bukata.

Wakilin mu Tidjani Moustapha Mahdi ya aiko mana da wannan rahoto.

An bukaci Idris Deby da ya dauki mataki akan miyagun akidu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.