Isa ga babban shafi
Najeriya

Yadda aka cafke Kwamandan Boko Haram a Ondo

'Yan sandan Jihar Ondo ne suka cafke Kwamandan Boko Haram Ibrahim Babawo
'Yan sandan Jihar Ondo ne suka cafke Kwamandan Boko Haram Ibrahim Babawo S Martin/Flickr
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 Minti

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kama daya daga cikin kwamandojin kungiyar Boko Haram da ke cikin jerin sunayen wadanda aka wallafa hotunansu da rundunar sojin ke nema ruwa a jallo.

Talla

‘Yan sandan Jihar Ondo ne suka cafke Kwamandan na Boko Haram a lokacin da suke bincike, kamar yadda Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman Kukasheka ya shaidawa RFI Hausa.

Kukasheka ya ce ana kiran dan Boko Haram din a matsayin Ibrahim Babawo wanda ake wa lakabi da Idiko ko kuma Na-gada kuma shi ne mai lamba 165 a cikin jerin ‘yan Boko Haram 200 da suke nema ruwa a jallo.

‘Yan sandan Ondo sun cafke Babawo ne a ranar Lahadi sannan suka mika shi ga rundunar Soji a Akure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.