Isa ga babban shafi
Najeriya

Rabin makarantun Bokon Borno na ci gaba da kasancewa a rufe

Tambarin Hukumar Unicef
Tambarin Hukumar Unicef
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
1 Minti

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya ce har yanzu rabin makarantun Bokon jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da kasancewa a rufe sakamakon yadda ‘yan Boko Haram suka lalata saura sannan kuma suka tilasta wa jama’a kaurace wa yankin.

Talla

Unicef ta ce sama da makarantu 1.400 ne ‘yan Boko Haram suka lalata, yayin da suka kasha malamai 2.295 daga shekara ta 2009 zuwa yanzu.

Har ila yau ayyukan kungiyar ta Boko Haram sun tilasta wa kananan yara milyan daya wadanda mafi yawansu dalibai ne suka bar jihar ta Borno a wannan mudda.

Ko baya ga rashin malamai da kuma lalacewar makarantun, rashin tsaro ya tilasta wa milyoyin mutane tserewa daga jihar ta Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.