Kamaru

Kamaru ta tsaurara tsaro a yankin renon Ingila

Kamaru ta tsaurara Tsaro a yankin masu magana da Ingilishi
Kamaru ta tsaurara Tsaro a yankin masu magana da Ingilishi STRINGER / AFP

Kamaru ta tsaurara tsaro a yankin renon Ingila bayan mutuwar mutane akalla 17 a rangama tsakanin jami’an tsaro da masu fafutikar samarwa yankin ‘yancin kai.

Talla

Jami’an tsaro sun rufe manyan hanyoyi da shingayen bincike a garin Buea bayan mutanen yankin kudu masu gabashin Kamaru sun ayyana cin gashin kai.

Sannan jami’an tsaron sun kakkafa shingayen bincike a garin Douala.

Kungiyar Amnesty International ta zargi Jami’an tsaron Kamaru da kasha fararen hula a yankin kasar da ke Magana da harshen ingilishi.

A ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba, ‘yan a waren na Kamaru suka kaddamar da sabuwar kasar Ambazonia mai cin gashin kai daga sauran yankin Kamaru renon Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.