Bakonmu a Yau

Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan Rashawa a Najeriya

Sauti 03:19
Kotun Koli a Najeriya
Kotun Koli a Najeriya nigerianpilot.com

Wata Kotu a Najeriya ta yankewa tsohon shugaban Cibiyar Bincike da bunkasa ayyukan noma da ke Ibadan Farfesa Benjamin Ogunmodede hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari saboda karkata kudaden da suka kai naira miliyan 177 daga cikin kasafin kudin Cibiyar da aka bashi. Wannan na daga cikin hukunci masu tsauri da aka yankewa wani babban jami’in gwamnati. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru shugaban Majalisar gudanarwar jami’ar man fetur da ke Warri.