Najeriya

Nadin manyan jami'ai a babban bankin Najeria CBN

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattawan kasar da wasikar neman izininta domin nada wasu manyan jami’ai a Babban Bankin kasar CBN.

Talla

Daga cikin wadanda shugaban ke son nadawa sun hada da Aishah Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan bankin.

Har ila yau akwai wasu mutane hudu da shugaban kasar ya nemi amincewar majalisar domin nada su a matsayin mambobin kwamitin tsara siyasar kudade a bankin na CBN.

 

Mutanen su ne Adeola Adenikinju,  Aliyu Sanusi,  Robert Asogwa da kuma Asheikh Maidugu, wadanda da zarar majalisar ta amince, mutanen za su fara aiki ne a cikin watan janairu mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.