Najeriya

An sake samun faruwar hatsarin jirgin ruwa a Yawuri

Wasu kwale-kwale a kan kogi
Wasu kwale-kwale a kan kogi AFP PHOTO / RIJASOLO

Rahotanni daga Jihar Kebbi a Najeriya sun tabbatar da sake samun wani mummunar hadarin jirgin ruwa a garin Yauri a yammacin ranar alhamis, kuma har zuwa wayewar gari wannan juuma’a  ba’a san adadin  wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hadarin ba.

Talla

Kwanaki biyu da suka gabata ne wani hatsari makamancin wannan ya auku inda mutane kusan 20 suka mutu sakamakon kifewar kwale-kwalen da suke ciki.

Wani mazauni garin na Yauri Alhaji Dan Asabe Mai Fata Yawuri, ya ce har cikin daren jiya an ci gaba da bincike domin gano wadanda lamarin ya rutsa da su a wannan karo.

 A Yawuri, kamar sauran garuruwa da ke yankin, jama’a na amfani jiragen ruwa ne domin gudanar da zirga-zirga da kuma sufuri sakamakon rashin gadoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.