Nijar

Rashin ingancin kamfanonin sadarwa a Nijar

Tauraron dan adam na sadarwa
Tauraron dan adam na sadarwa (

A Jamhuriyar Nijar ,hukumar ARTP dake da nauyi sa ido kan ayyukan kamfanonin sadarwa masu zaman kan su ta dau mataki na ladabtar da wasu kamfanonin sadarwa na kasar guda hudu tareda tilasta masu biyan tara na kudi saboda rashin biyan bukata ga yan kasar.

Talla

Daga cikin kamfanonin da wannan hukunci ya shafa akwai kamfanin sadarwa na Faransa Oranga da zai biyan tara na kudi cfa milyan 925 da 474, Sahel Com da tara na kudin cfa milyan 620 da 505 na kudin cfa, Moov milyan 423 sai Airtel kamfanin sadarwa malakar kasar Indiya a Nijar zai biyan tara mai nauyi na kudin cfa bilyan 1 da milyan 576.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.