FIFA

Kasashen Afrika da ke hanyar tsallakewa zuwa Rasha

Sénégal da Morocco da Tunisia sun fi fatar tsallakewa zuwa Rasha
Sénégal da Morocco da Tunisia sun fi fatar tsallakewa zuwa Rasha RFI / Pierre René-Worms

Bayan Nigeria da Masar sun samu nasarar shiga sahun kasashen da za su buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi. Yanzu Tunisia da Senegal da Morocco ke kan layi na fatar cike gibin gurbin na Afrika.

Talla

Kasashe 5 za su wakilci Afrika a gasar cin kofin duniya a Rasha

Tunisia na fuskantar barazana domin Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo na iya tsallakewa a rukuninsu na A.

Cote d’Ivoire na iya hanawa Morocco tsallakewa a rukuninsu na C.

Maki daya Morocco ta ba Cote d’Ivoire, kuma sai wasan karshe za a tantance tsakaninsu.

Tunisia dai na neman maki guda ne kacal a karawar da za ta yi da Libya.

Idan har Tunisia ta sha kasha, kuma DRC ta doke Guinea to zai kasance mai yawan kwallaye ne tsakaninsu zai tafi Rasha.

Rukunin da babu tabbas shi ne na D, domin Senegal da Burkina Faso da Cape Verde da Afrika ta Kudu dukkaninsu na da hasken zuwa Rasha.

Amma Senegal ta fi fatan samun nasara domin tana neman maki 2 a karawar karshe da za ta yi da Afrika ta kudu.

Burkina faso ce ta biyu da maki 6, haka ma Cape Verde tana da maki 6 a matsayi na uku, Afrika ta kudu ce ta karshe a rukunin.

A ranakun 6 da 14 ga Nuwamba ne kasashen za su fafata domin tantance sauran wadanda za su wakilci Afrika bayan Najeriya da Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.