Isa ga babban shafi
malawi

Mayu sun tilasta wa ma'aikatan MDD ficewa a Malawi

Ana yawan samun rade-radin maita a Malawi, kasar da ke da karancin masu ilimi
Ana yawan samun rade-radin maita a Malawi, kasar da ke da karancin masu ilimi Getty Images/Bob Elsdale
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun fice daga yankin kudancin Malawi saboda fargabar mayu da ake rade-radin cewa suna tsotse jinin mutane.Shugaban kasar Peter Muthurika ya lashi takobin gudanar da bincike mai zurfi bayan wannan lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai.

Talla

Gwamnatin Malawi ta lashi takobin gudanar da bincike bayan ‘yan kato da gora sun kashe mutane bakwai ta hanyar yankar rago saboda zargin cewa, suna dauke da maita.

Ana zargin mutanen da aka kashe da kokarin neman jinin da za su tsotse daga jikin dan adam da sunan tsafi.

Hukumomin kasar sun sanya dokar hana fitar dare, in da aka takaita zirga-zirgar jama’a daga karfe bakwai na safe zuwa biyar na yamma.

Majalisar Dinkin Duniya wadda ke taimakawa wajen samar da abinci da bunkasa ayyukan gona a Malawi, ta janye ma’aikatanta daga yankin da ake fama da wannan matsala saboda tsaro.

Duk da dai ba a kai hare-hare kan ma’aikatan na Majalisar Dinkin Duniya, amma ta bukace su da komawa birnin Blantyre mai tazarar kilomita 90 daga in da ake fama da fargabar mayun.

A wani rahoto da Kamfanin Dillancin Labaran AFP ya samu kwafinsa, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ta dakatar da duk wata ziyara a yankin saboda tashin hankalin.

Sai dai shugaban kasar, Peter Mutharika ya ce, sun kaddamar da bincike mai zurfi don gano tushen lamarin.

Malawi dai na fama da rade-radin maita kuma akwai karancin ilimi tsakanin mutanen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.