Najeriya-tattalin arziki

Arzikin Najeriya zai bunkasa kasashen kudu da sahara-IMF

Ginin kamfanin mai na NNPC a Najeriya
Ginin kamfanin mai na NNPC a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Hukumar bada lamuni ta duniya IMF ta yi hasashen cewa tattalin arzikin kasashen kudu da sahara zai bunkasa da kusan kashi uku da rabi sakamakon farfadowar tattalin arzikin Najeriya a fannin fetir da ayyukan noma.

Talla

Hasashen rahoton na IMF ya ce, Najeriya za ta samu ci gaban tattalin arziki da kusan kashi 1 a bana, haka kuma zai kai kusan kashi biyu a badi.

Najeriya ta fuskanci tabarbarewar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin mai, al’amarin da ya datse yawan kudaden da kasar ke samu.

A dayan bangaren kuma, rahoton na IMF ya ce, za a samu ci gaba a fannin mai a Angola, in da aka samu sauyin shugabanci bayan kawo karshen mulkin shekaru 38 na Eduardo dos Santos.

Amma hasashen ya nuna rashin tabbas a Afrika ta Kudu saboda rikicin siyasar jam’iyya mai mulki ta ANC.

Sannan rahoton ya yi gargadin cewa za a fuskanci karancin abinci da fari a kasashen Gambia da Sudan ta Kudu da kuma Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.