Kenya

Kenya: ‘Yan sanda sun yi arangama da magoya bayan Raila Odinga

Magoya bayan Odinga sun gudanar da zanga-zanga a Kenya
Magoya bayan Odinga sun gudanar da zanga-zanga a Kenya REUTERS/Thomas Mukoya

Mutane kusan 20 suka jikkata a zanga-zangar da ‘yan adawa suka kaddamar a Kenya a yau Laraba, kwana guda bayan jagoransu Raila Odinga ya sanar da janyewa daga zaben shugaban kasa da ake shirin sakewa tsakanin shi da shugaba Uhuru Kenyatta.

Talla

Dubban mutane ne suka fito zanga-zangar a yankin Kisumu da jaghoran adawa Raila Odinga ke da yawan magoya baya.

Masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi tare da kone tayoyi da kuma jifar motocin mutane da duwatsu.

Lamarin da ya sa ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa su.

Wannan dai na zuwa bayan jagoran adawa Raila Odinga ya sanar da janyewa daga zaben shugaban kasa da ake shirin sake gudanarwa a ranar 26 ga watan oktoban bayan soke zaben 8 ga watan Agusta da aka bayyana shugaba Uhuru Keyatta a matsayin wanda ya yi nasara.

Zanga-zangar 'Yan adawa a Kenya
Zanga-zangar 'Yan adawa a Kenya REUTERS/James Keyi

Odinga dai ya ce bai yadda da baki-dayan tsarin zaben ba wanda har zai bada damar gudanar da sahihin zabe, lamarin da ya sa ya sanar da dakatar da takararsa.

Yanzu kuma Odinga na son a sake lallen shirin zaben.

Farfesa Habu Muhammad kan zaben Kenya na ranar 26 ga watan Oktoba da kotu ta sake sanyawa a yau.

Yanzu dai babu tabbas kan ko zaben da za a sake zai yiyu a Kenya, kodayake babbar kotun Kasar ta ba dukkanin ‘yan takarar da suka shiga zaben farko da ya gabata damar shiga sabon zaben da za a sake.

Raila Odinga yayin sanar da janyewa daga zaben kenya da za a maimaita

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.