Togo

'Yan adawar Togo sun bijirewa haramcin zanga-zanga

'Yan adawar Togo sun shirya gagarumin zanga-zanga a mako mai zuwa
'Yan adawar Togo sun shirya gagarumin zanga-zanga a mako mai zuwa Reuters

‘Yan Adawa a kasar Togo sun ki janye shirinsu na gudanar da zanga-zanga guda biyu a makon gobe duk da haramcin da gwamnatin kasar ta sanar.

Talla

Jam’iyyu 14 suka yi kira ga magoya bayan su da su shiga zanga zangar a ranakun laraba da alhamis na makon gobe domin ci gaba da matsin lamba ga shugaba Faure Gnassingbe na ganin ya kawo karshen mulkin sa.

Eric Dupuy, kakakin Jam’iyyar National Alliance For Change ya ce zanga zangar ta ranar laraba zata karkare ne a gaban Majalisar Dokoki.

Ministan kula da yankunan kasar Payadowa Boukpessi ya ce an haramta gangamin siyasa tsakanin litinin zuwa Juma'a na makon gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.