Kamaru

'Yan Boko Haram 58 sun mika wuya ga hukumomin Kamaru

Rundunar Sojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram
Rundunar Sojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Rahotanni daga Kamaru na cewa, kusan mutane 60 da suka ce, Boko Haram ta tilasta mu su shiga yakin da ta ke yi a Najeriya, sun mika wuya ga hukumomin kasar.

Talla

Bayan shafe shekaru biyu da kungiyar, mutanen sun yanke shawarar tserewa da iyalansu tare da mika kansu ga hukumomin Kamaru.

Mutanen dai sun shaida wa manema labarai cewa, lallai sun taimaka wa Boko Haram a yakinta amma a yanzu sun ajiye makamansu bisa ratsin kansu.

Boko Haram ta yi garkuwa da jumullar mutane 400 ‘yan asalin Kamaru da suka hada da maza 58 da mata 86 da kananan yara 244.

Boko Haram ta sace mutanen ne bayan ta kai hare-hare kan kauyukansu, in da daga bisani ta shigo da su Najeriya don agaza ma ta wajen kai farmaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.